11 Mayu 2020 - 05:45
Sarakunan Bahrain Sun Dakatar Da Wani Taro Na Masu Adawa Da Yin Hulda Da HKI

Sarakunan kasar Bahrain sun bada umurnin dakatar da wani taron na yin allawadai da maida hulda da Haramtacciyar kasar Isra’ila wanda ake gudanarwa ta shafukkan sadarwa na yanar gizo a jiya Asabar 9 ga watan Mayu na wannan shekara.

(ABNA24.com) Sarakunan kasar Bahrain sun bada umurnin dakatar da wani taron na yin allawadai da maida hulda da Haramtacciyar kasar Isra’ila wanda ake gudanarwa ta shafukkan sadarwa na yanar gizo a jiya Asabar 9 ga watan Mayu na wannan shekara.

Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta bayyana cewa “Kungiyar Matasan democrdiyya ta kasar Bahrain” tare da hadin guiwa da “kungiyar yaki da maida hulda da haramtacciyar kasar Isra’ila” ita ma ta kasar ta Bahrain ne, suka shirya taron.

Labarin ya kara da cewa ana cikin tsakiyar taron ne, wani jami’in a ma’aikatar ayyuka da kuma lamuran zamantakewa ta kasar ya kira masu gudanar da taron ta wayar tarho, inda ya bada umurnin dakatar da taron da kuma gargadin cewa umurnin daga manya-manyan jami’an masarautar kasar ce.

Wannan dai, ya nuna a fili irin shirye–shiryen da masarautar kasar ta Bahrain ta ke yi na maida huldan jakadanci da haramtacciyar kasar Isra’ila a bayyane ko kuma a hukumance.


/129